Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA – ya habarta cewa, kakakin rundunar sojin kasar Irakin ya bayyana cewa: Sansanin Ain al-Assad da ke lardin Al-Anbar yana karkashin cikakken ikon dakarun kasar.
Ya kara da cewa, "Babu wata rundunar yaki daga rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa ko NATO a sansanin Ain al-Assad, kuma masu ba da shawara ne kawai ke halartar wajen ba da tallafin kayan aiki da taimako ga sojojin Iraki."
Ya kara da cewa: Da yawa daga cikin wurare da ke cikin sansanin sojojin kasashen waje ne gaba daya suka fice, kuma wasu daga cikin sansanonin ana amfani da su ne kawai wajen kai kayan aiki ga sojojin Iraki da suka hada da makamai da motoci da kayan aiki domin gudanar da aikin tsaro ga dakarun mu suna masu taimakawa sosai.
Kakakin rundunar sojin Irakin ya ci gaba da cewa: Wannan sansanin na Iraki da kuma kare shi alhakin sojojin Iraki ne, har ma masu ba da shawara suna samun goyon bayan Irakin ne.
Tun da farko dai, kawancen kungiyar Fatah, daya daga cikin kungiyoyi na siyasa a Iraki, ya bayyana cewa, janyewar sojojin kasashen waje ba wai kawai Amurka ba ce, za ta hada da dukkanin sojojin da ke kawance da kasashen duniya.
A baya dai rundunar hadin gwiwa ta Iraki a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce dakarun hadin gwiwar kasa da kasa za su fice daga Iraki a karshen wannan wata.
A cewar rahotanni da aka fitar a watannin da suka gabata, bisa labaran da aka nakalto daga jami'an Iraki da na Amurka da aka watsa su, bangarorin biyu sun amince a tattaunawar da suka yi da Washington da Bagadaza kan manyan tsare-tsare na cewa dukkan sojojin Amurka za su fice daga Iraki a ranar 31 ga Disamba, 2021.
342/